Ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bukaci masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da su kai tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar zuwa yankin kudancin kasar a zaben 2027.
Wike ya bayyana haka ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da yake karanta sanarwar bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar.
A cikin sanarwa ya ce dole ne a mutunta tsarin dimukradiyya da kundin mulkin jam’iyyar wajen bai wa wanda ya fito takara daga yankin Kudu dama,idan aka yi duba da yadda aka bai wa yankin Arewa dama a zabukan da suka gabata.