Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi watsi da sanarwar taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 100 da jam’iyyar PDP ta shirya gudanarwa a ranar 30 ga Yuni, tana mai cewa sanarwar ta saba ka’idoji.
A wata wasika da INEC ta aike wa jam’iyyar, mai dauke da sa hannun mataimakiyar sakatariyar hukumar, Hajiya Hau’ru Aminu, an bayyana cewa sanarwar bata cika sharuddan da ke sashe na 2(12)(3) na dokokin jam’iyyun siyasa na 2022 ba, wanda ke bukatar shugaban jam’iyya na kasa da sakataren jam’iyya su sanya hannu tare.
INEC ta shawarci PDP da ta bi ka’ida wajen gabatar da irin wannan sanarwa a nan gaba. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da rikice-rikice ke ci gaba da ruruwa a cikin jam’iyyar.