Majalisar dattijai ta mika kudirin dokar sake fasalin haraji zuwa ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu domin amincewa da aiwatarwa.
Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai, Sanata Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a lokacin wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Talata.
A shekarar da ta gabata ne shugaba Tinubu ya gabatar da kudirori hudu kan tsarin haraji domin tantancewa. Bayan dogon muhawara, majalisun biyu sun amince da su.
Sanata Adaramodu ya tabbatar da cewa majalisa ta kammala aikinta kuma yanzu ta mika kudirin zuwa fadar shugaban kasa don daukar mataki na karshe.