Gwamnan Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya amince da sake fasalin hukumar gudanarwa ta ƙungiyar ƙwallon kafa ta Kano Pillars, tare da naɗa tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin sabon Babban Manajan ƙungiyar.
Wannan sauyi na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin farfaɗo da martabar ƙungiyar Kano Pillars, yayin da take shirin shiga sabuwar kakar gasar Nigeria Premier Football League (NPFL) ta shekarar 2025/2026.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Juma’a, ta bayyana cewa an yanke wannan hukuncin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallon kafa, biyo bayan ƙarewar wa’adin hukumar da ta gabata wanda ya ɗauki shekara guda.
Sabuwar hukumar gudanarwar da aka ƙaddamar na da mambobi 17, inda Ali Muhammad Umar (Nayara) zai jagoranci hukumar a matsayin Shugaba, tare da sauran mambobi, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.