Ministan Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya Nyesom Wike, ya bayyana cewa yana da kudi tun kafin ya shiga siyasa.
Ya ce, sabanin wanda ya gada, Rotimi Amaechi, wanda ya ce ya fito daga gidan talakawa, shi kuma ya fito daga gidan masu hali.
Ministan ya kuma amsa cewa yana da motar alfarma kirar Rolls-Royce wadda ya saya da kudinsa.
Wike ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a Channels TV, yayin da yake mayar da martani kan zargin cin hanci da Amaechi ya yi masa.