Ministan Abuja, babban birnin tarayyar Nijeriya Nyesom Wike, ya kare salon rayuwarsa da kuma mallakar motar alfarma ta Rolls Royce, yana mai jaddada cewa dukiyarsa ba ta fito daga mukamin gwamnati ba, sai dai daga kyakkyawan asalin danginsu masu hali.
Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television, Wike ya karyata zarge-zargen cin hanci da almubazzaranci, yana mai cewa babu wanda zai iya rayuwa ba tare da kudi ba, kuma son kudi ba yana nufin mutum mai rashawa ba ne.
Wannan martani ne ga tsohon Gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, wanda ya taba tambayar daga ina Wike ya samo wannan dukiya, musamman ikon sayen motar Rolls Royce a lokacin da yake rike da mukamin gwamnati.