Fadar Shugaban Ƙasa ta shawarci mambobin sabuwar gamayyar jam’iyyu da aka kafa ƙarƙashin tutar jam’iyyar ADC da su manta da zaɓen 2027, su mayar da hankali kan zaɓen 2031.
A ‘yan kwanakin da suka gabata ne wasu ’yan adawa ciki har da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar; tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark; tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Mr Peter Obi; da kuma tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da wasu, suka haɗu a birnin Abuja inda suka bayyana jam’iyyar ADC a matsayin dandalin gamayya domin ƙwace mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Sai dai mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Sunday Dare, ya shawarci waɗanda ke jagorantar gamayyar da su jira, su gwada sa’ar su ne bayan Shugaba Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu.
Sunday Dare ya yi wannan magana ne a Abuja yayin da yake mayar da martani kan damuwar da ake nunawa game da yiwuwar gamayyar ta ƙwace mulki daga gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta.