Majalisar Dattawan Nijeriya ta gindaya wasu sharudda kafin ta dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kan kujerarta, bayan wata kotun tarayya da ke Abuja ta soke dakatarwar watanni shida da majalisar ta yi mata.
A hukuncin da ta yanke a ranar Juma’a, Mai shari’a Binta Nyako ta umurci Majalisar Dattawan da ta dawo da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, inda ta bayyana dakatarwar a matsayin mai tsanani da ya wuce kima.
Da yake mayar da martani kan hukuncin, mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce ba za a dawo da Sanata Natasha kai tsaye ba.
Adaramodu ya bayyana cewa hukuncin kotu bai soke ikon tsarin kundin tsarin mulkin da ke ba Majalisar Dattawa damar ladabtar da mambobinta ba.
Ya kara da cewa Majalisar za ta sake zama domin tattauna batun ne kawai bayan Akpoti-Uduaghan ta cika umarnin kotu.