Jam’iyyar ADC reshen jihar Zamfara ya sanar da fara zawarcin Gwamna Dauda Lawal da sauran ‘yan siyasa masu nagarta a jihar na su shiga jam’iyyar, gabanin zaben 2027, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
Da yake magana da manema labarai a Gusau babban birnin jihar, Shugaban jam’iyyar Kabiru Garba, ya bayyana cewa jam’iyyar ta karbi sabbin mambobi sama da 100 daga wasu jam’iyyu daban-daban cikin kwanaki goma da suka gabata, yana mai cewa sauyin sheka da aka samu ƙarfafa guiwa ne ga jam’iyyar.
Ya bayyana fatarsa cewa karin ‘yan siyasa daga jam’iyyun APC da PDP za su shiga ADC nan ba da jimawa ba a jihar Zamfara, yana jaddada cewa kofar jam’iyyar a bude take ga duk wanda ke da nagartaccen hali a siyasa da kuma kishin ingantaccen mulki na ya zo ya shiga.