Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta dage wajen shawo kan matsalolin tsaro masu tsanani da ta gada.
Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekaru 50 da kammala karatu na dalibai karo na 18 a kwalejin horar da hafsan sojoji ta Nijeriya (Nigerian Defence Academy, NDA) da aka gudanar a Abuja.
Ya ce a shekarar 2022, Nijeriya ta kasance a mummunan mataki na hadari, tana fama da dumbin kalubale da suka yi barazana ga hadin kan kasa, zaman lafiya da makoma.
Ya bayyana cewa kalubalen sun hada da matsalar ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas, kashe-kashe da hare-hare a Arewa maso Yamma, rikice-rikice a yankin Neja Delta da kuma tashe-tashen hankula na ‘yan awaren kafa kasa a Kudu maso Gabas.
A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta dauki matakai masu karfi wajen dawo da tsaro da kuma gina sabon kwarin gwiwar kasa.