Mata da matasan al’ummar Bendeghe Ekiem da ke ƙaramar hukumar Etung a Jihar Cross River sun ba Kwamishinan Noma, Johnson Ebokpo, wa’adin kwanaki 14 da ya janye shirin sayar da gonar gwamnati da ake shirin yin ruf da ciki, ko kuma su kasance cikin shiri don ganin mata sun yi tsirara su fita su yi rawa a cikin gonar koko.
An yanke wannan shawara ne a ranar Asabar yayin wata zanga-zanga da matasa da mata na al’ummar suka shirya domin nuna rashin jin daɗinsu game da batun.
A wata hira da jaridar PUNCH shugabar mata ta al’ummar, Ntunkai Obi, da kuma jagorar mata Helen Ogar, sun roƙi kwamishinan da ya tuntubi shugabannin al’ummar don su tattauna a kan batun, domin a tantance matakin da ya kamata a ɗauka na gaba.