Fitaccen malamin addinin Musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa tafiyarsa zuwa ƙasar Turkiyya ba ta da alaka da barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan yiwuwar kai hari a Nijeriya saboda zargin kisan Kiristoci.
Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa, bayan da hotunan Sheikh Gumi suka bayyana yana cikin ƙasar Turkiyya, wasu mutane a kafafen sada zumunta sun yada labarin cewa malamin ya gudu ne don tserewa hare-haren da ake zargin Amurka za ta kai Nijeriya.
Wasu masu amfani da dandalin X sun yi tsokaci suna cewa Gumi na iya zama cikin wadanda za su fuskanci hare-haren Trump, kasancewar an taba ganinsa yana tattaunawa da wasu ’yan bindiga a dazuka.
Sai dai Sheikh Gumi ya ce ya dade yana shirin tafiya tun kafin wannan barazana ta Trump.



