Kungiyar Nigeria Unite ta kai karar minista Nyesom Wike zuwa ga Kungiyar Tarayyar Turai
Ministan Abuja Nyesom Wike ya dauko hanyar kassara dimukuradiyya a Nijeriya. Wannan shi ne babban zargin da ke cikin wata zungureriyar wasika da ƙungiyar ta “Nigeria Unite” ta gabatar ga shugabar hukumar gudanarwa ta Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen. Kungiyar mai rajin kare dimukuradiyya ta nuna tsananin damuwa cewa dimokuradiyya a Nijeriya na dab da rugujewa — tare da zargin cewa Ministan Abuja, Barrister Nyesom Wike, na mamaye siyasa da karya tsarin mulkin Nijeriya.
A cikin wasikar da aka aika ranar 11 ga Nuwamba 2025, ƙungiyar ta ce halayen Wike da goyon bayan da yake samu daga gwamnatin tarayya sun jefa Nijeriya cikin hanyar zama ƙasar jam’iyya ɗaya, lamarin da ke shafar dimokuradiyya gaba ɗaya a kasashen yankin Sahel.
A cewar wasikar, Wike ana zarginsa da:
damfarar tsarin siyasa,
tsoratar da ‘yan adawa,
sayen hukumomi da alkalai,
murƙushe jam’iyyun PDP, LP da ADC,
kulle ofisoshin jam’iyyun adawa da amfani da albarkatun gwamnati don rushe su,
da kuma amfani da ’yan sanda, wasu alkalan tarayya, da ma’aikatan INEC wajen murde tsarin siyasa.
Wasikar ta ce dabi’un ministan na Abuja sun kai ga samar da :
rabuwar kawuna a tsakanin ‘yan majalisar Rivers saboda rikicinsa da Gwamna Sim Fubara,
ƙone majalisar dokoki da rikice-rikicen doka,
tilasta wa gwamnoni, sanatoci da manyan jam’iyyun adawa shiga APC,
da kuma karkatar da dimokuradiyya zuwa salon mulkin kama-karya.
Ƙungiyar ta gargadi cewa yadda “APC ke amfani da barazana, cin hanci, da cin zarafi don murƙushe adawa” na nuna cewa Nijeriya na dab da zama ƙasar jam’iyya ɗaya — abin da ka iya haifar da tarzoma da tashin hankali kafin zaɓen 2027.
Wasikar ta da kungiyar Nigeria ta aike wa kasashen Turai ta kuma zargi Majalisar Dokokin Nijeriya da zama mai “rauni kuma a ƙarƙashin ikon shugaba Tinubu,” ta ce rashin sa hannun su wajen tsare doka da oda ya ƙara buɗe ƙofa ga zalunci da karya tsarin mulki.
A cikin buƙatunta, ƙungiyar Nigeria Unite ta roƙi Tarayyar Turai, Majalisar Dinkin Duniya, Amurka da Birtaniya su sa baki cikin lamarin, su sanya takunkumi kai tsaye kan Nyesom Wike, da kuma wasu alkalan da ake zargi suna taimaka masa.
Wasikar ta yi gargadin cewa duk wata rugujewar dimokuradiyya a Nijeriya — ƙasa mai mutane miliyan 250 — ka iya haifar da girgizar siyasa da tsaro a yammacin Afirka, ta ƙara yawan kwararar ’yan gudun hijira, ta kuma haifar da barazana ga Turai da Amurka.
A ƙarshe, ƙungiyar ta ce lokaci ya yi da kasashen duniya ya kamata su tashi tsaye domin “kare dimokuradiyya kafin lamarin ya rikide ya zama abin tsoro.


