Hukumomin Libiya sun kori ’yan Nijeriya 80 daga ƙasar bayan kama su suna zama ba bisa ƙa’ida ba, a wani yunkuri na rage cinkoso a cibiyoyin da ake tsare masu aikata irin laifin.
Hukumar yaki da masu shiga kasar ba bisa ka’ida ba tare da haɗin gwiwar ofishin jakadancin Nijeriya da ke Tripoli ne suka jagoranci mayar da su ta filin jirgin sama na Mitiga International Airport a ranar Laraba.
Kungiyar Migrant Rescue Watch, wadda ke sa ido kan walwalar ’yan ci-rani a Libiya, ta bayyana cewa an kora mutanen ne bisa umarnin kotu da hukumar ’yan sanda ta fitar.



