Majalisar dattawan Nijeriya na shirin amincewa da kudurin da zai haramta daukar mutane ‘yan ƙasa da shekaru 18 a aikin soja.
Sanata Abdulaziz Yar’Adua daga Katsina ne ya gabatar da kudurin, wanda ke neman soke tsohuwar dokar soji ta 2004 tare da kawo sabuwar doka da ta dace da tsarin mulki da harkokin tsaro na zamani.
A yayin gabatar da kudurin, Sanata Yar’Adua ya ce tun da jimawa ake da bukatar gyaran, domin dokar da ake amfani da ita yanzu ta samo asali ne daga umarnin soja, wanda bai dace da tsarin dimokuraɗiyya ba.
Ya ce sabuwar dokar za ta kawo canje-canje da dama, ciki har da tsaurara hukunci ga manyan laifukan soja, kare kotunan soja daga tsoma bakin manyan jami’ai, da tabbatar da cewa ƙwararrun lauyoyin soja za su iya kare rundunar a kotunan fararen hula.



