Dakarun haɗin gwiwa na “Operation Hadin Kai” sun dakile wani yunkurin garkuwa da masu yi wa kasa hidima 74 a hanyar Buratai zuwa Kamuya, jihar Borno.
Mai magana da yawun rundunar, Manjo Sani Uba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis, inda ya ce sojojin sun yi gaggawar kai dauki bayan motocin ɗaliban sun lalace a wurin da ake yawan yin garkuwa da mutane.
A cewar sa, masu yi wa kasa hidimar maza 36 da mata 38, motar tasu ta lalace ne da misalin ƙarfe 9:05 na dare a ranar Talata.
Sojojin sun gano matasan suna cikin haɗari, suka garzaya suka kwashe su zuwa sansanin soja da ke Buratai don kare su daga yiwuwar hare-haren ‘yan ta’addan.



