Rundunar da ke gudanar da binciken manyan laifuka a ƙasar Kenya (DCI) ta tabbatar da kama wasu ’yan Nijeriya uku bisa zargin aikata damfara ta yanar gizo.
Jaridar Punch ta rawaito cewa, jami’an DCI sun kama mutanen ranar Laraba, bayan al’ummar yankin sun shigar da korafi kan motsin mutanen da suke gani a daren cikin wani gida da basu amince da shi ba.
DCI ta bayyana cewa mutanen uku sun ce suna gudanar da kasuwanci na intanet, sai dai an gano cewa suna zaune ne a kasar ba bisa ka’ida ba, kuma ba tare da samun lasisin aiki a kasar ba.



