Dubban likitoci a Ingila sun fara yajin aiki na kwanaki biyar a ranar Juma’a saboda rashin gamsuwa da albashi da kuma karancin guraben horaswa, lamarin da ya janyo tsaikon ayyuka a asibitocin da ke fadin kasar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, wannan shi ne karo na 13 da likitocin ƙasar ke yin yajin aiki tun daga watan Maris din shekarar 2023.
Yajin aikin ya shafi ma’aikatan asibiti da ke kasa da kwararrun likitoci, wadanda su ke da kusan rabin yawan likitocin da ke aiki a asibitocin gwamnati.



