Rahotanni sun tabbatar da cewa a daren Laraba ne Shugaba Paul Biya ya rattaba hannu kan wata sabuwar doka ta sauya jami’ai a makarantar tsaro ta kasar ta Kamaru (International School of Security Forces).
Sabon sauyin ya shafi sassa daban-daban na makarantar, ciki har da sashen nazari, cibiyar bincike da tattara bayanai, da kuma sashen gudanarwa.
A cikin shekara guda kacal, Shugaba Biya mai shekara 92 ya yi sauyin manyan hafsoshin soja fiye da sau shida, tun bayan shekarar 2023 lokacin da juyin mulki ya yi kamari a kasashen yankin Sahel da ma makwabciyarsu Gabon.



