Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake nada Janar Mohammed Buba Marwa mai ritaya a matsayin shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a sabon wa’adi na shekaru biyar, wanda zai kai shi har zuwa shekarar 2031.
Marwa dai ya fara aikin a matsayin shugaban hukumar ne tun a Janairun 2021 bayan nadin da tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari ya yi masa.
Marwa, wanda dan asalin jihar Adamawa ne kuma tsohon soja, ya halarci makarantar horas da sojoji (NDA), ya kai mukamin laftanar a shekarar 1973.



