DCL Hausa Radio
Kaitsaye

’Yan bindiga sun sake kai hari a Kano tare da yin garkuwa da mutane 11

-

’Yan bindiga sun sake farmakar wani kauye a jihar Kano, inda suka yi garkuwa da mutane 11 a Unguwar Tsamiya (Dabawa), da ke ƙaramar hukumar Shanono.

Rahotanni daga mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na daren Litinin, inda maharan suka dinga harbe-harbe ta sama tare da dukan wasu daga cikin mutane kafin su yi awon gaba da mutum 11, maza tara da mata biyu sannan suka yi awon gaba da shanu biyu.

Google search engine

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa lamarin ya faru ne kwanaki kalilan bayan wani farmakin da aka kai ‘Yan Kamaye a ƙaramar hukumar Tsanyawa, wani yanki da ke iyaka da jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Sarkin Musulmi ya bukaci gwamnoni da su rika sauraron masu sukarsu

Sarkin ya bayyana haka ne a taron Gwamnonin Arewa da majalisar sarakunan gargajiya da aka gudanar a Kaduna a Litinin din nan, Sarkin Musulmi ya...

‘Yan bindiga sun saki matashi da mata da suka sace a Abuja

'Yan bindiga sun saki wani yaro mai shekaru 15 da kuma ’yan mata shida da suka yi garkuwa da su a kauyen Gidan Bijimi da...

Mafi Shahara