Rundunar ’yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da mutuwar mutane 33 sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a Bui da ke karamar hukumar Arewa ta jihar.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Bashir Usman, ya bayyana cewa bincike ya nuna maharan na shigowa yankin ne daga karamar hukumae Gudu da ke jihar Sokoto State.
Ya ce bayan harin, mazauna ƙauyukan Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal da Dan Mai Ago sun tashi tsaye domin kare kansu, abin da ya jawo artabu mai tsanani da ya yi sanadin mutuwar mutane 33.
A cewar sa ’yan sandan tare da sojoji da sauran hukumomin tsaro sun ƙara tura jami’ai da kayan aiki zuwa yankin, tare da ci gaba da sintiri domin dawo da zaman lafiya da hana sake faruwar irin wannan hari.



