Home Sabon Labari An saci jaririya ‘yar watanni 6 a Kano

An saci jaririya ‘yar watanni 6 a Kano

157
0

An kama wata mata da ake zargi da safarar mutane da wata jaririya mai kimanin watanni 6 da haihuwa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da ke birnin Kano.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa an kama matar ne a ranar Lahadi, a lokacin da take kokarin hawan jirgi don zuwa birnin Legas.

Ma’aikatan hukumar kula da filayen jirgin sama ne suka kama matar, sannan suka hannanta ta ga ‘yan sanda don su ci gaba da bincike.

An dai ta kokarin jin ta bakin kai magana da yawun rundunar ‘yansandan jihar Kano Abdullahi Haruna, amma haka bata cimma ruwa ba, kasancewar duk wayoyinsa a kashe.

Sai dai ko a ranar 11 ga watan Oktoba, 2019 sai da rundunar ‘yansandan jihar ta Kano ta ba da sanarwar ceto wasu yara 9 da aka yi zargin an sace.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply