DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Saturday, October 10, 2026
HomeLabarai'Yan bindiga sun nemi N20m kan kowane mai yi wa kasa hidima...

‘Yan bindiga sun nemi N20m kan kowane mai yi wa kasa hidima da suka sace a Kogi

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da wasu masu yi wa kasa hidima (NYSC) kwanaki uku da suka gabata a jihar Kogi sun bukaci a biya kudin fansa har naira miliyan 20 a kan kowane mutum daya.

Lamarin ya faru ne a lokacin da matasan ke kan hanyarsu ta komawa Abuja daga jihar Bayelsa bayan kammala kwas din horaswa na makwanni uku a sansanin ‘yan bautar kasa, inda maharan suka tare su a kan babbar hanyar Aloma zuwa Egane da ke karamar hukumar Ofu a jihar Kogi.

Wani dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace ya bayyana cewa maharan sun tuntubi iyalan yarinyar tare da gabatar da bukatar kudin fansar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyar, “Daya daga cikin ‘ya’yanmu da aka sace a kan hanyarsu ta dawowa Abuja daga jihar Bayelsa bayan kammala sansanin horaswa na makwanni uku, masu garkuwar sun bukaci a biya naira miliyan 20 a matsayin kudin fansa.”

Wannan batu na zuwa ne bayan da rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta tabbatar da sace fasinjojin ciki har da masu yi wa kasa hidimar a kan wannan hanya.

Rundunar ta bayyana cewa hadin gwiwar jami’an tsaro ya yi nasarar kubutar da mutum 11, ciki har da direbobin motocin guda biyu da lamarin ya shafa, yayin da ake ci gaba da aikin ceto sauran wadanda ke hannun ‘yan bindigar.

A halin da ake ciki, iyalan wadanda aka sacen sun yi kira ga gwamnatin tarayya, mahukuntan shirin NYSC, da kuma hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen ganin an kubutar da ‘ya’yansu cikin koshin lafiya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata