Home Kasashen Ketare Shugaba Isufu Mahamadu na jimamin sojojin Nijar da suka rasa ransu

Shugaba Isufu Mahamadu na jimamin sojojin Nijar da suka rasa ransu

91
0

A wata sanarwar ce da ya fitar a shafinsa na Facebook shugaban kasar jamhuriyar Nijar Alhaji Isufu Mahamadu ya yaba wa kokarin sojojin kasar na fatattakar ‘yan ta’addar da suka kai ma wani sansanin sojin kasar da ke Chinegodar a cikin jihar Tillaberi hari.

Shugaba ya bayyana cewa ” ina so in yi jinjina da yabama jami’an tsaron mu tare da abokan huldarmu da suka yi nasarar fatattakar wannan mahara. Da sunan dukkan ‘yan Nijar nake mika sakon ta’azziyata ga dangin dakarun da suka hadu da ajalinsu kuma nake fatan Allah koro da manzan sauki ga wanda suka jikkata”

Shima a nashi shugaban kasar Burkina Faso ya taya al’ummar Nijar din da ma takwaranshi wannan juyayi ta shafinsa na yanar gizo.

To sai dai a nasu waje al’ummar kasar suma na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu akan wannan hari inda wasu ma ke kira da a canza salan yakin da ‘yan ta’adda

Wasu al’ummar dai na kira ga gwamnatin da ta yi duk mai yiwuwa dan ayita ta kare da ‘yan ta’addar wajen ba ma sojojin umarnin shiga farautar ‘yan ta’addar dan karewa, kuma idan dai har gwamnatin da gaske take wajen yakar ‘yan ta’addar to ta kara zage damtse.

Wannan hari dai ya wakana ne a kasa da mako guda kafin a bude wani taro dan tattaunawa kan matsalar tsaron dake damun yankin Sahel da zai hada shuwagabannin yankin da takwaransu na kasar Faransa Emmanuel Macron a birnin Peau na kasar ta Faransa da ake sa ran zai huddo mahuta akan matsalolin tsaron da yankin ke fama da ita.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply