DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Tuesday, October 6, 2026
HomeLabarai'DSS na son dakatar da shari'ar Sowore sai bayan zaben 2027'

‘DSS na son dakatar da shari’ar Sowore sai bayan zaben 2027’

Hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (DSS) ta umarci lauyanta, Akinlolu Kehinde (SAN), da ya nemi a dage shari’ar da ake yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, kan zargin laifukan yanar gizo har sai an kammala babban zaben shugaban kasa na 2027.

Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa hukumar ta dauki wannan mataki ne domin ba Sowore damar gudanar da yakin neman zabensa ba tare da fuskantar wata tangarda daga zaman kotu ba, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

Rikicin ya samo asali ne daga rubuce-rubucen da Sowore ya wallafa a shafukansa na X da Facebook a ranar 25 ga watan Agustan 2025, inda ya bayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin “mai laifi” (criminal).

Lamarin ya sa DSS ta ba shi wa’adin kwanaki bakwai ya goge rubutun, kuma rashin yin hakan ya sa hukumar ta maka shi a Babbar Kotun Tarayya a watan Satumban 2025 domin neman fassarar doka kan ko ya halatta a kira shugaban kasa ko wani mutum da wannan lafazi.

Ko da yake DSS ta shigar da kamfanonin Meta da X a cikin karar da farko, kotu ta cire kamfanonin sadarwar tare da barin Sowore a matsayin wanda ake tuhuma shi kadai. Sowore ya sha musanta zargin da ake masa a karkashin dokar laifukan yanar gizo ta 2024, yana mai bayyana shari’ar a matsayin wata manufa ta siyasa da nufin tauye masa ‘yancin fadar albarkacin baki.

Majiyar ta kara da cewa Babban Daraktan DSS, Tosin Ajayi, ya gana da lauyoyin hukumar a ranar 20 ga watan Agusta jim kadan bayan hukumar zabe ta ƙasa (INEC) ta ba da damar fara yakin neman zabe, inda ya bayyana cewa adalci ne a dakatar da shari’ar na tsawon watanni hudu domin ba shi damar shiga zabe yadda ya kamata.

Ana sa ran lauyoyin na DSS za su sanar da Babbar Kotun Tarayya wannan matsaya a hukumance a ranar Litinin, 14 ga watan Satumban 2026, a lokacin da kotun za ta dawo daga hutun shekara-shekara.

A halin yanzu, Sowore, wanda a baya kotun ta bayar da belinsa, zai ci gaba da gudanar da ayyukansa na siyasa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata