Home Labarai Tsaro na kara inganta a Katsina – Gwamnati

Tsaro na kara inganta a Katsina – Gwamnati

166
0

Gwamnatin jihar Katsina ta ce tsaro na kara inganta bakin gwargwado a jihar duba da yadda jami’an tsaro ke tarwatsa mafakar ‘yan ta’adda a sassan da ke fama da karancin tsaro.

Mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro Alh Ibrahim Ahmad ya yi wannan furucin a lokacin taron manema labarai da ya gudana a Katsina.

Yace irin ayyukan da jami’an tsaron ke gudanarwa da yadda jama’ar gari ke ba su hadin kai wajen samar da bayanan sirri, ne ya sa ake samun wadannan nasarori.

Alh Ibrahim Ahmad yace yanzu haka an mafiyawan mutane sun koma aikin gonakinsu gadan-gadan wanda a baya ya nemi ya gagare su.

Mai ba gwamnan shawara ya ce kada mutane su gajiya wajen ba da bayanan sirri da za su taimaki gwamnati da jami’an tsaro wajen gudanar da aikin inganta tsaro.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply