Ministan lafiya na Nijeriya Dr Osagie Ehanire, ya ce cutar corona ta yadu a kananan hukumomi 586 cikin 774 da ake da su a kasar.
Dr Ehanire ya bayyana haka ne bayan kammala taron majalisar zartaswa ta kasa a Abuja.
A rahoton Freedom Radio Kano, Ministan ya bayyana damuwarsa ganin yadda har yanzu cutar ke ci gaba da yaduwa, kuma tattalin arziki na gurgunta.
