Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi ‘Yan Nijeriya sama da milyan 199 nada wayar salula – NCC

‘Yan Nijeriya sama da milyan 199 nada wayar salula – NCC

139
0

Shugaban hukumar sadarwa ta Nijeriya Prof. Umar Danbatta ya ce yanzu haka mutanen da suka samu damar mallakar wayar hannu ta salula a Nijeriya ya karu daga milyan 184 a Disambar bara, zuwa milyan 199.3 a watan Mayun, 2020.

Umar Danbatta na magana ne a wajen taron ba da lambar yabo da NCC ta shirya a Abuja.

Ya ce yawan masu saka “data” ya karu mutane milyan 126 zuwa 147.1. Sai masu saka katin kallon talabijin shi ma ya karu daga mutane milyan 72 zuwa milyan 80.2.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply