DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeSiyasa'Ba dan siyasar da zai iya dawo da tallafin fetur, yaudara ce'

‘Ba dan siyasar da zai iya dawo da tallafin fetur, yaudara ce’

Jam’iyyar APC mai mulki ta yi fatali da kiraye-kirayen dawo da tallafin man fetur, inda ta gargadi ’yan Nijeriya da su kiyayi ’yan siyasar da ke daukar alkawarin sauya matakan tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka.

Darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a 2027, Sanata Abdulaziz Yari, ya bayyana cewa duk dan siyasar da ke yakin neman zabe da alkawarin dawo da tallafin man fetur yana yaudarar al’umma ne.

Sanata Yari ya bayyana hakan ne a lokacin da mambobin kwamitin ayyuka na kasa (NWC) na jam’iyyar suka kai masa ziyara, a matsayin martani ga alkawarin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya yi na dawo da tsarin tallafin mai idan ya lashe zaben 2027.

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya jaddada cewa tsarin tallafin man fetur ya lakume kudaden da suka wuce kima ba tare da samun abin da ake buƙata ba, yana mai cewa dawo da shi zai sake jefa kasar cikin mawuyacin hali.

A cewar Yari, ko a kasafin kudin shekarar 2023 da majalisar dokoki ta amince da shi kafin Shugaba Tinubu ya kama aiki a watan Mayun waccan shekarar, babu wani tanadi da aka yi wa tallafin man fetur din.

“Duk wanda ke cewa zai dawo da wannan tallafi, yana yaudarar kansa ne, yana kuma yaudarar al’ummar Nijeriya baki daya,” in ji Yari.

Ya kara da cewa a lokacin da yake shugabancin kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF), sun shafe shekaru hudu suna kalubalantar kamfanin NNPC domin ya fitar da ainihin alkaluman yawan man da ake sha a kasar a kowace rana, amma hakan ya faskara har sai da aka rika ikirarin cewa Nijeriya na biyan tallafin man ne ga yankin yammacin Afirka baki daya.

Sanata Yari ya jaddada cewa yakin neman zaben jam’iyyar APC na 2027 zai mayar da hankali ne wajen kare kyakkyawan aikin da gwamnatin Tinubu ta yi ta hanyar amfani da sahihan bayanai da alkaluma, maimakon cin zarafin abokan hamayya.

Ukashatu Wakili
Ukashatu Wakilihttps://dclhausa.com
Ukashatu Wakili is a journalist and media professional serving as Deputy Managing Editor and Internship Coordinator at DCL Hausa. He has extensive experience in broadcast and digital journalism, with expertise in news reporting, editorial production, newsroom coordination and journalist training. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata