Home Labarai Hajjin 2019: za a fara jigilar maido da alhazan Nijeriya.

Hajjin 2019: za a fara jigilar maido da alhazan Nijeriya.

82
0

Daga Abdullahi Garba Jani

A ranar Asabar 17 ga watan Agusta, 2019 ne hukumar kula da aikin hajji ta kasa -NAHCON- ta sanar da cewa za ta fara aikin jigilar alhazan Nijeriya daga kasar Saudi Arabia.

Kwamishinan hukumar mai kula da aikace-aikace, Malam Sale Modibbo ne ya ba da tabbacin hakan a lokacin da suka kammala taron bayan hawan Arafa da ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan aikin hajjin bana a birnin Makka.

Ya ce kamfanonin jiragen sama na MaxAir da Flynas ne za su fara aikin kwaso alhazan, bayan da aka kafa kwamitocin da za su tabbatar da gudanar da aikin ba tare da matsala ba.

Wasu Alhazan Nijeriya

A gefe guda kuma shugaban kwamitin majalisar dattawa ta Nijeriya kan harkokin kasashen waje Muhammad Bulkachuwa, ya shaida wa jaridar Daily Nigerian cewa hukumar-NAHCON ta yi kyakkyawan shirin maido da alhazan .

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply