Home Labarai NNPC na gina asibitin ₦21bn a Katsina

NNPC na gina asibitin ₦21bn a Katsina

86
1

Kamfanin matatar mai na Nijeriya NNPC ya fara gina asibitin kula da cutuka masu yaɗuwa a jihar Katsina.

Shugaban kamfanin Mele Kyari ya ƙaddamar da ginin asibitin mai gadaje 200 a Kaita, ranar Asabar.

Asibitin wanda za a kashe Naira Biliyan ₦21bn wajen aikin sa, zai riƙa kula da marasa lafiya daga yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.

Kuma yana ɗaya daga cikin asibitoci 12 da NNPC zai gina a shiyyoyi 6 na Nijeriya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here