Home Labarai Tsohuwar data koka an hana ta kaiwa Buhari fura ta tsinci dame...

Tsohuwar data koka an hana ta kaiwa Buhari fura ta tsinci dame a kala

1141
2

A cikin makon nan ne muka kawo muku labarin yadda wata tsohuwa mai suna Ladi da ke karamar hukumar Sandamu a jihar Katsina, inda take bayyana rashin jin dadinta akan yadda aka kasa yi mata hanya ta gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda ta saba zuwa su yi zumunci tun Kafin ya zama Shugaban Nijeriya.

Korafin Ladi Sandamu dai ya isa kunnen Dan madamin Daura Alhaji Musa Haro wanda yana daga cikin makusanta Shugaban kasa, ya kuma yi mata sha tara ta arziki, inda ya aika mata kudi kimanin
Naira 250,000 da atamfofi guda 5 da kuma buhun shinkafa 3.

Shin ko burin Ladi Sandamu zai cika na ganin Shugaba Buhari?

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here