Home Kasashen Ketare Amurka: Za a cire sunan Shugaba Wilson saboda wariyar launin fata

Amurka: Za a cire sunan Shugaba Wilson saboda wariyar launin fata

106
0

Jami’ar Princeton ta kasar Amurka za ta cire tare da sauya sunan tsohon Shugaban kasar Amurka Woodrow Wilson da ta sanya a wani sashe na jami’ar saboda kasancewar shi mai akidar nuna wariyar launin fata.

Wannan matakin dai ya biyo bayan zanga-zanga da akayi a fadin kasar ta Amurka saboda kisan da wani dansanda ya yi wa bakar fatar nan mai suna George Floyd.

Woodrow Wilson shi ne ya shugabanci Amurka daga shekarar 1913 zuwa 1921.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here