Home Coronavirus Adadin masu Corona ya zarta miliyan 10 a duniya

Adadin masu Corona ya zarta miliyan 10 a duniya

67
0

Adadin mutanen da ke dauke da cutar corona ya haura milyan 10 a fadin Duniya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa kuma mai bin diddigin masu dauke da cutar Corona ya bayyana cewa zuwa yanzu kimanin mutane 1,300,000 ne suka mutu a fadin Duniya.

Kasar Amurka dai ita ce kan gaba na adadin masu dauke da cutar ta Corona a Duniya, inda adadin masu dauke da cutar ya kai Miliyan 2 da rabi.

Zuwa yanzu dai kimanin mutane Dubu 360 ne suka kamu a nahiyar Afirika, ya yin da 9,300 suka rasa ransu a fadin nahiyar Afirika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here