Home Coronavirus Corona: An ja kunnen gwamnatin Neja kan bude makarantu

Corona: An ja kunnen gwamnatin Neja kan bude makarantu

157
0

Kungiyar malamai ta kasa reshen jihar Neja ta ja hankalin gwamnatin jihar kar ta yi garajen bude makarantu a fadin jihar.

Mataimakin Sakataren kungiyar kwamared Labaran Garba ne ya bada wannan shawara ya yin taron da kungiyar ta jagoranta a birnin Minna.

Ya kara da cewa ya zama wajibi ga malamai da su kare kansu daga kamuwa daga cutar corona domin kada su kai ga yada ta ga dalibansu.

A karshe ya bayyana cewa kungiyar ta kashe kimanin Naira Miliyan 150 wajen ginin sakatariyar ta ta zamani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here