Home Labarai Buhari zai dora harsashin shimfida bututun iskar gas

Buhari zai dora harsashin shimfida bututun iskar gas

54
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai dora harsashin shimfida bututun iskar gas da zai taso daga Ajaokuta ya bi ta Kaduna ya zarce jihar Kano akan kudi dala milyan $2800.

Za a gudanar da bikin kaddamarwar ne a fadar Shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Haka nan kuma za a gudanar da wasu bukukuwan irin wannan a yankin Rigacikun da ke jihar Kaduna da kuma harabar kamfanin mulmula karafa na Ajaokuta da ke jihar Kogi.

A cikin wata sanarwa da kamfanin mai na kasa ya fitar, ta yi bayanin cewa ana sa ran kammala aikin cikin shekaru 2.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here