Home Coronavirus COVID-19: An janye dokar hana zirga-zirgar jihohi a Nijeriya

COVID-19: An janye dokar hana zirga-zirgar jihohi a Nijeriya

161
0

Gwamnatin Nijeriya ta janye dokar hana zirga-zirga tsakanin jihohi daga ranar 1 ga watan Yuli sai dai dokar ta ce banda lokutan da aka hana fita.

Shugaban kwamitin da Shugaban kasa ya kafa na yaki da annobar Corona kuma Sakataren gwamnatin tarayya Mr Boss Mustapha ne ya tabbatar da haka a Abuja.

Shugaba Buhari ne dai ya ba da wannan umurnin hakan bayan yin nazarin kan rahoto na 5 da kwamitin ya bayar.

Tuni dai dama gwamnatin kasar ta ba da umurnin ci gaba da zirga-zirgar jiragen samar kasar a cikin gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here