Home Labarai Ya kamata hankulan jama’a su karkata fannin tsaro – Sarkin Daura

Ya kamata hankulan jama’a su karkata fannin tsaro – Sarkin Daura

159
0

Mai martaba Sarkin Daura Alhaji Dr Umar Farouk Umar ya tunatar da ‘yan kasar nan akan da su karkatar da hankulansu kan matsalar tsaro da ta addabi wasu sassa a fadin Nijeriya dama yadda za su ba da gudunmawa wajen ganin an dakile al’amuran rashin tsaro a fadin kasar baki daya.

Sarkin na Daura ya yi wannan kiran ne ya yin wata ziyara da Shugaban rundunar sojin kasar nan Lt Tukur Yusuf Burutai ya kai masa a fadar Daurama.

Sarkin ya kara da yin kira da a yi amfani da matakan da aka dauka a baya irin na kirkirar ‘yansandan gimbiya da aka yi amfani da shi wajen dakile yakin basasa da ya gudana a kasar nan.

A karshe ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi mulkin kasar nan a daidai lokacin da ta ke cikin mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here