Home Taskar Guibi Taskar Guibi: 01.07.2020

Taskar Guibi: 01.07.2020

97
0

Assalamu alaikum barkanmu da asubahin laraba, tara ga watan Zulkida, shekarar 1441 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da daya ga watan Yuli, shekarar dubu biyu da ashirin.

1. Yau daya ga watan Yuli, ma’aikatan gwamnatin tarayya bangaren ilimi na ci gaba da korafin an shiga sabon wata ba labarin dilin-dilin.

2. Yau daya ga watan Yuli da ya kamata talakan Nijeriya ya soma biyan sabon kudin zama a duhu, sai dai ‘yan majalisar dokoki ta tarayya sun tsaya masa, an fasa karin sai watanni uku na farko na shekara mai zuwa ta 2021.

3. Yau daya ga watan Yuli, yau ce ‘yan ajin karshe na firamare, da karamar sakandare, da babban sakandare za su koma makaranta domin shirye-shiryen jarabawa.

4. Yau daya ga watan Yuli jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin shimfida bututun iskar gas daga Ajakuta zuwa Kano da wasu kamfanonin kasar Sin wato Caina biyu suka samar da kudaden gudanar da aikin rance, daga bisani a biya su.

5. Yau daya ga watan Yuli a jiya kasar Sin wato Caina ta gano wata sabuwar cutar wato SWINE FLUE (suwainfulu) cuta da ake dauka daga aladu da take tunanin ita ma za ta yi kisa shigen na kwaronabairos.

6. Yau daya ga watan Yuli Babban Bankin Nijeriya ya ce zai tallafa wa manoma su fiye da miliyan daya da rance na kudi da kayan aikin gona.

7. Yau daya ga watan Yuli jiya aka damke wasu Canisawa biyu da suka kulle ma’aikatansu ‘yan Nijeriya a kamfaninsu da ke Abuja tun watan Fabrairu na shekarar nan ba shiga ba fita, wai tsoron kada su debo musu kwaronabairos daga waje zuwa cikin kamfanin.

8. Yau daya ga watan Yuli jiya gwamnan jihar Ondo Rotimi ya sanar da ya harbu da kwaronabairos.

9. Yau daya ga watan Yuli jiya aka yi musayar yawu da karamin ministan kwadago Keyamo, da zaman hadin gwiwa na kwamitocin kwadago da samar da aiki, na majalisar dattawa da ta wakilai a kan sai ya ba su tsarin da ma’aikatarsu ta yi don daukar ‘yan Nijeriya su dubu dari bakwai da saba’in da hudu aiki, shi kuma ya ce ba zai bayar ba, saboda zargin idan ya ba su, inasu-inasu za su dauka kawai, ba za su bari ‘ya’yan talakawa su samu aikin ba kamar yadda aka dade ana zargin sanatoci da ‘yan majalisar wakilai na yi.

10. Yau daya ga watan Yuli a jiya dakarun soja suka sanar da sun kashe wasu ‘yan bindiga su hudu a jihar Taraba.

11. Yau daya ga watan Yuli jiya dakarun ofareshan – gama-aiki ta sama suka kai wa wasu bandis da ke jihar Neja farmaki.

12. Yau daya ga Yuli jiya kotu ta yi fatali da wata kara da Dino Melaye ya kai a kan wani kudiri na dokar da ta shafi cututtuka masu yaduwa.

13. Yau daya ga watan Yuli jiya ‘Yan sanda sun sanar da kama wani kidinafa da ya karbi naira miliyan bakwai da rabi kudin fansa, ya kuma kashe wanda aka biya shi kudin fansar tasa.

14. Yau daya ga watan Yuli, ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin tun watan Afrilun bara da aka kara albashi suke zaman jiran ariyas, ga shi har watan Afrilu na wannan shekarar ya zo ya wuce, an shiga Mayu, da Yuni, da Yuli ba amo ba labari.

15. Yau daya ga watan Yuli wasu malaman jami’o’i na gwamnatin tarayya na ci gaba da korafin rabonsu da albashi tun na watan Janairun shekarar nan.

16. Yau daya ga watan Yuli jiya kafin in kwanta bacci akwai sabbin harbuwa da kwaronabairos su dari biyar da sittin da daya a jihohi da alkaluma kamar haka:

Legas 200
Edo 119
Kaduna 52
Abuja 52
Neja 32
Ogun 19
Ondo 16
Imo 14
Filato 11
Abiya 8
Oyo 8
Bayelsa 7
Katsina 6
Kano 5
Bauci 3
Oshun 3
Kabbi 3
Barno 2
Jigawa 1

Jimillar wadanda suka harbu 25,694
Jimillar da suka warke 9,746
Wadanda suka riga mu gidan gaskiya 590
Wadanda ke jinya 15,358

Mu wayi gari lafiya.

Af! Yau daya ga watan Yuli, jiya na ji a rediyo wasu matan fulani da ake hira da su, suna cewa bafulatani dan halas musamman su fulani da aka san su da kunya, ba ya kashe wani balle uban da ya haife shi. Suka ce a bi diddigin fulanin da ke sana’ar kisa, za a gano cewa wajen yawon tallar nono da matan fulani ke yi, suka jajibo cikinsu, suka haife wa mazajensu na aure a ruga. Suka girma suka hana kowa sakat.

Is’haq Idris Guibi
Kaduna Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here