Home Kasashen Ketare An cimma matsayar ranakun babban zabe a Nijar

An cimma matsayar ranakun babban zabe a Nijar

118
2

Hukumar zabe ta Nijar CENI ta sake saka wata sabuwar ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomi.

A ya yin wani zaman da ta yi a ranar Talata, hukumar tsara zaben ta bayyana ranar 13 ga watan Disamba mai zuwa a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomin kafin daga bisani a gudanar da na shugaban kasa da ‘yan majalisa ranar 27 ga watan dai na Disambar.

A baya dai hukumar zaben ta ce ba za a gudanar da zaben kananan hukumomin ba har sai an yi na shugaban kasa da ‘yan majalisar, lamarin da ya haifar da tada jijiyoyin wuya daga wasu jam’iyyun siyasa, musamman ma ‘yan adawa da ma wasu jam’iyyu gungun masu mulki.

To sai dai, ganin irin yadda hakan ya janyo kace-nace wasu rahotanni ke cewa shugaban kasa da kanshi ya nemi hukumar ta yi kokarin saka ranar da za ta kawo karshen wannan dambarwa.

Da dai, hukumar zaben ta bayyana cewa za a gudanar da zaben kananan hukumomin ne a ranar 1 ga watan Oktoba nan kafin daga bisani ta ce matsalar cutar corona ta tilasta mata dage ranar zuwa 17 ga Janairun 2021 kafin zuwa wannan sanarwa ta karshe da kuma hukumar sasanta jam’iyyun siyasa ta kasa (CNDP) za ta gabatar ma jam’iyyun siyasar a ya yin zaman da za ta yi a nan gaba.

2 COMMENTS

Leave a Reply