Home Labarai An gano malaman makaranta na bogi 443 a Benue

An gano malaman makaranta na bogi 443 a Benue

57
0

Gwamnatin jihar Benue ta ce ta gano malaman makaranta na bogi da ke cikin tsarin albashin jihar su 443.

Bugu da kari, gwamnatin ta gano mutane 18 da suka mutu ake biyansu albashi, 70 da suka ajiye aiki, sai 193 da aka sauya wa wurin aiki.

Shugaban hukumar kula da malaman makaranta ta jihar Dr Frank Kyungun ne ya sanar da hakan a lokacin mika rahoton tantance malaman makaranta ga gwamna Samuel Ortom a Makurdi.

Dr Kyungun ya ce an gano wadannan malaman bogin bayan tantance ma’aikata 4,473 na hukumar a jihar.

Leave a Reply