Home Labarai Fani Kayode: Sarkin Shinkafi ya aminta da ajiye rawunnan ‘yan majalisarsa 5

Fani Kayode: Sarkin Shinkafi ya aminta da ajiye rawunnan ‘yan majalisarsa 5

128
0

Mai martaba sarkin Shinkafi Muhammad Makwashe Isah, ya amshi takardun ajiye mukaman ‘yan majalisarsa 5.

‘Yan majalisar sarkin sun ajiye mukamansu ne don nuna rashin gamsuwa da sarautar da sarkin ya ba wa tsohon ministan sufurin sama Femi Fani Kayode.

Idan za a iya tunawa dai, a makonnin da suka gabata, sarkin ya nada Fani Kayode sarautar “Sadaukin Shinkafi”, batun da ya jawo cece-kuce a ciki da wajen jihar.

Bayan ba da wannan sarsuta ne, Bilyaminu Yusuf, Sardaunan Shinkafi; Umar Ajiya, Dan Majen Shinkafi, Hadiza Abdul’aziz Yari, Iyar Shinkafi, Dr Tijjani Salihu Shinkafi, Uban Marayun Shinkafi da Dr Sulaiman Shu’aibu, Sarkin Shanun Shinkafi, suka mika takardar ajiye rawunnansu don nuna rashin amincewarsu da nadin Femi Fani Kayode.

Leave a Reply