Home Labarai Sadaukin Shinkafi: An maye gurbin wadanda suka ajiye rawunnansu

Sadaukin Shinkafi: An maye gurbin wadanda suka ajiye rawunnansu

141
0

Mai martaba sarkin Shinkafi a jihar Zamfara Muhammad Makwashe Isah ya maye gurbin wadanda suka ajiye rawunnansu biyo bayan nadin sarautar da ya yi wa tsohon Ministan sufurin sama Femi Fani Kayode.

A cikin wata takarda daga Ibrahim Muhammad, Sarkin Sudan Shinkafi ta ce sarkin ya amince da nadin Aliyu Jibril Guraguri a matsayin Sardaunan Shinkafi da Umar Abdullahi a matsayin Dan Majen Shinkafi.

Sauran su ne Bello Hassan Shinkafi a matsayin Uban Marayun Shinkafi da Dr Usman Muhammad a matsayin Sarkin Shanun Shinkafi.

Leave a Reply