Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamna Chukwuma Soludo murna bisa sake lashe zaben gwamnan jihar Anambra, yana mai cewa nasarar da ya samu ta tabbatar da irin jagoranci na gari da yake gudanarwa.
A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fita, Tinubu ya ce nasarar Soludo a zaɓen da aka gudanar ranar Asabar ta sanya shi zama gwamna na uku a tarihin siyasar jihar da ya yi nasara a wa’adi na biyu.
Tinubu ya kuma yaba wa al’ummar jihar,jami’an tsaro da hukumar zaɓe INEC bisa yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana da kwanciyar hankali.



