Home Labarai Zaɓen ƙananan hukumomi: an bada hutu a jihar Bauchi

Zaɓen ƙananan hukumomi: an bada hutu a jihar Bauchi

78
0

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, ya ayyana ranar Juma’ar nan 16 ga watan Oktoba a matsayin ranar hutu, a shirye-shiryen gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a jihar da za a yi ranar Asabar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka gwamnan kan harkokin yaɗa labarai Mukhtar Giɗaɗo ya fitar.

A cewar sanarwar, an bada hutun ne domin ba jama’ar jihar damar gudanar da zaɓen da za a yi a dukkan ƙananan hukumomin jihar 20.

Leave a Reply