Home Coronavirus An saka ranar komawa jami’ar UMYUK

An saka ranar komawa jami’ar UMYUK

225
0

Hukumar gudanarwar jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua da ke Katsina ta saka ranar Litinin 19 ga watan Oktoba, 2020 a matsayin ranar da za a koma jami’ar.

A wata sanarwa daga magatakardan jami’ar, ta ce ga daliban da ba su kammala rajistar su ba, za su ci gaba daga ranar 19 zuwa 30 ga watan Oktoba,2020.

Takardar ta ce za a gudanar bikin marhabin da sabbin dalibai a ranar 27 ga watan Oktoba, 2020.

Sai dai mahukuntan jami’ar sun shawarci dalibai, malamai da sauran ma’aikatan jami’ar da su rika lura da matakan da aka gindaya don gudun kamuwa ko yada cutar corona.

Leave a Reply