Home Labarai A ci gaba da kulle boda har sai shekara mai zuwa ta...

A ci gaba da kulle boda har sai shekara mai zuwa ta 2020- Shugaba Buhari

82
0

Abdullahi Garba Jani

Shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya amince da a kara tsawaita rufe boda har sai 31 ga Janairu, 2020.

Wannan umarni na cikin matakan karfafa shirin rufe boda mai lakabin “sintiri kan iyakokin kasa” ya hada da jami’an tsaro daban-daban.

Sakon hakan na kunshe ne a cikin wata takarda daga mataimakin shugaban hukumar kwastan mai kula da sashen bincike Victor Dimka.

Takardar da ta fito daga fadar shugaban kasa na dauke ne da lamba NCS/ENF/ABJ/221/S.45 da kwanan wata na 1 ga Nuwamba, 2019.

Takardar ta ce yin hakan zai sa a kara samun nasarorin da aka samu ta dalilin rufe kan iyakokin Nijeriya.

A cikin takardar an ba jami’an tsaron da ke gudanar da wannan shiri na killace kan iyakoki tabbacin cewa za a biya su alawus-alawus dinsu kamar yadda ya dace.

A ranar 20 ga watan watan Agusta, 2019 ne, shugaba Buhari ya ba da umurnin a rufe kan iyakar Nijeriya da kasashe makwabta.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply