Home Coronavirus A cikin kwana biyu ba a samu ɓullar Covid-19 ba a Kano

A cikin kwana biyu ba a samu ɓullar Covid-19 ba a Kano

116
0

Rahotanni daga jihar Kano sun nuna cewa ba a samu ɓullar cutar coronavirus ba a cikin kwanaki biyu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun yawaitar mace-mace daga wata baƙuwar cuta a ƴan kwanakin nan.

Gwamnatin jihar dai ta alaƙanta mace-macen ne dai zazzaɓin malaria da ciwon suga, yayin da hukumar lafiya ta jihar ta sanar da mutum biyu da suka mutu sakamakon Covid-19 da yammacin jiya Litinin.

Saidai kuma a jawabin da hukumar NCDC ta gudanar na ɓarkewar cutar a ranakun 26 da 27 ga watan Maris, ya nuna cewa ba a samu rahoton wanda ya kamu da cutar ba ko ya mutu a jihar ta Kano.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply