Home Lafiya A dakatar da taruwar jama’a – Gwamnonin Nijeriya

A dakatar da taruwar jama’a – Gwamnonin Nijeriya

74
0

Gwamnoni 36 na Nijeriya sun bada shawarar hana duk wani nau’i na taruwar jama’a, a matsayin wani mataki na hana yaduwar coronavirus a cikin kasar.

Sun kuma kafa wani kwamiti karkashin kulawar majalisar kula da tattalin arziki wanda zai lalubo hanyoyin da gwamnatin tarayya da na jihohi za su magance illar da wannan cuta za ta haifar ga tattalin arziki.

Kwamitin dai zai kasance karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, tare da gwamnonin Jigawa, Edo, Ebonyi, Nasarawa, Kaduna, Kebbi da kuma Ogun a matsayin wakilai.

Wata sanarwa da ta fito daga mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa Laolu Akande, da ya fitar yau a Abuja, ya ce wannan mataki na hana taruwar mutane ya zo ne a lokacin taron da majalisar ta gudanar a fadar shugaban kasa jiya Alhamis.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply